By Abbas Yakubu Yaura
Gamayyar kungiyoyin matasa a jihar Nasarawa karkashin inuwar kungiyar matasan Najeriya ta amince da tsohon Gwamna kuma Sanata mai wakiltar Nasarawa ta kudu a majalisar dokokin kasar Umaru Al-Makura a matsayin shugaban jam’iyyar APC na kasa.
Da yake jawabi a taron manema labarai a ranar Litinin a Lafiya, Shugaban NYCN na Jihar, Jaafar Loko, ya bayyana cewa sun amince da Al-Makura ne saboda gagarumin ci gaban da ya samu a matsayin Gwamnan Jihar daga shekarar 2011 zuwa 2019.
Yayin da yake bayyana cewa kungiyoyin matasan ba su da alaka da kowace jam’iyya, Loko ya ci gaba da cewa, matasan kananan hukumomin jihar 13 sun yanke shawarar amincewa da Al-Makura a matsayin shugaban jam’iyyar APC ne saboda irin ayyukan da ya yi na karfafa matasa a tsawon shekaru.
Ya ce, “Mun yanke shawarar daukar wannan matsayi ne saboda irin nasarorin da Al-Makura ya samu a siyasance a lokacin da yake rike da mukamin shugaban matasa a jam’iyyar ta kasa kuma a matsayin gwamnan jihar Nasarawa tsakanin shekarar 2011 zuwa 2019.
“Lokacin da yake Gwamna, matasa ne suka taka rawa a cikin shirin na jihar, kuma ya samu damar kafa tsarin karfafa matasa na Jihar Nasarawa, wanda ya sa yawancin matasanmu suka samu aikin yi, da dai sauran ayyukan da suka dace.
“Ba mu da tantama Sanata Al-Makura ya mallaki kyawawan halaye da cancantar jagorantar jam’iyyar APC a matakin kasa.
“Muna kira ga daukacin ‘ya’yan jam’iyyar APC da shugabannin kasar nan da su mara masa baya domin ya zama shugaban jam’iyyar na kasa.”