Gamayyar Ƙungiyar kudancin jihar Kaduna sun bazama a titunan birnin tarayya Abuja na dandalin taro na Unity Fountain dake birnin tarayyar.
Matasan sun ce sun fito wannan gangami ne don nuna fushin su game da matsalar tsaro da ta addabi yankinsu.
Matasan da suka fito karkashin inuwar gamayyar Ƙungiyar kudancin Kaduna, sun ce matsalolin sace sacen mutane da fashin daji da dukkannin sauran nau’ukan matsalar tsaro a Jihar ya isa haka.
Idan za a iya tunawa gwamnatin Jihar ta Kaduna ta bayyana cewa yan fashin daji sun yi sanadiyar salwantar rayukan Mutane sama da 200 da sace sama da 700 gamida jikkata karin wasu sama da 200 daga watan Afirelun wannan shekara kawai.
Masu Zanga-zangar na dauke da kwalaye ne dake nuna damuwoyi daban-daban da suks hada “ta’addanci ya isa haka a Kaduna’ dole gwamnatoci a dukkan matakai su farka’ el-Rufa’i yana barci da dai sauransu.
A yan baya-bayan nan dai Jihar Kaduna ta zamto wata cibiya ta zubda jini da sace sacen mutane lamarin da ya kai ga gwamnan jihar Mallam Nasir el-Rufa’i ya janye ƴaƴanshi daga makarantun gwamnatin jihar.