Bangaren matasa na jam’iyyar PDP, ya nuna damuwarsa kan cece-kucen da ake yi tsakanin dan takararta na shugaban kasa, Atiku Abubakar da gwamnan jihar Ribas, Nwesom Wike.
Sakataren kungiyar matasan jam’iyyar PDP a kasashen ketare, Kwamared Tochukwu Onah a wata sanarwar da aka rabawa manema labarai ya bayyana cewa, shirun da jam’iyyar PDP ta yi na kara ta’azzara lamarin saboda dimbin tambayoyin da ba a amsa ba wadanda ka iya kawo cikas ga damar jam’iyyar a zaben 2023 mai zuwa.
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Onah wanda shi ne shugaban daliban Najeriya a Australia ya jaddada bukatar shugabannin jam’iyyar su tabbatar da sulhu tsakanin Atiku da Wike wanda ya ce ya ci gaba da kasancewa a matsayin ginshikin jam’iyyar ko bayan faduwa zaben 2015.
Zan Jangoranci Fitar Da Najeriya Daga Kangin Duhun Da Take Fama Dashi — Atiku
“Gwamna Nyesom Wike shi ne ginshikin wannan babbar jam’iyyar tamu tun bayan 2015 jam’iyyar ta kusa mutuwa, ya tsaya takarar jam’iyyar tare da wasu masu kishin kasa kuma ya mai da ita babbar jam’iyyar adawa amma abin ya narke a gare shi ba a kira shi ba, bai dace ba kuma Ya kamata shugabannin jam’iyyar cikin gaggawa su yi sulhu da shi tare da sasanta sauran masu biyayya ga jam’iyyar.
“Mu matasan jam’iyyar PDP da ke kasashen waje, mun yi tir da yadda aka yi wa Gwamna Nyesom Wike, wanda ya yi kasada da ransa, ya kashe dukiyarsa, ya kuma yi fafutukar tabbatar da wanzuwar wannan jam’iyyar, don haka muna kira ga shugabannin babbar jam’iyyar mu da su yi abin da ya kamata wajen warware bambance-bambancen,” in ji shi.
Onah wanda aka sani da fadin gaskiya ga mulki yayi kira da shugaban jam’iyyar PDP na kasa Sen. Iyocha Ayu yayi murabus. Ya kara da cewa rashin adalci ne shugaban jam’iyyar ya fito daga Arewacin Najeriya tare da dan takarar shugaban kasa.