Wani mutum mazauni Singapore ya bukaci wata mata ta biya shi £1.9m kan yadda ta yi wasa da hankalinsa bayan kin amincewa da tayin soyayyarsa inda suka yi kawance na shekaru 4, Dailymail ta ruwaito.
K Kawshigan, darektan wani kamfani, ya maka kara kan Nora Tan Shu Mei bayan ta ki yarda da soyayyarsa inda ya ce hakan bacin suna ne a gare shi kuma rashin amincewarta ta janyo masa asarar rasa abokan kasuwanci akalla biyar.
KU KARANTA: Matashi ya tsunduma mahaifinsa cikin rijiya saboda fili
Ita ma ta maka shi kara inda ta nemi ya biya ta wasu kudade. Ta ce ta siya na’urar kallon wanda zai shigo daga kofa, da sauran na’urorin da za su kare ta daga matashin da ya dinga bibiyarta a ta son shi.
Kuma tana neman kusan £900 don mayar da asarar da ta yi. Kamar yadda Channel News Asia ta nuna, Kawshigan ya kai ta kara biyu inda ya ce sun rabu ne bayan ta sanar da shi cewa a matsayin aboki take kallonsa ba masoyi ba.
Ya ce ta keta dokar da suka sanya inda ta ce za ta duba yiwuwar inganta kawancensu zuwa soyayya. An dage sauraron karar zuwa ranar 9 ga watan Fabrairu don kammala jin ta bakunansu.
Matashi Mai Siyar Da Kwakwa Ya Koma Karatu Ƙasar Waje, Ya Samu Babban Matsayi a Cikin Turawa
Wani matashi mai suna Peter Bawuah, wanda ya kammala digirin sa a fannin kimiyyar siyasa a jami’ar kimiyya da fasaha ta Kwame Nkrumah, ya nuna irin gagarumin sauyin rayuwar da ya samu.
A shafin sa na TikTok, Peter ya sanya wani bidiyo wanda ya nuna yadda yake shan baƙar wahala a ƙauyen su na Techimantia inda yake sayar da kwakwa kafin ya samu gurbin zuwa karatu kyauta a ƙasar Canada. Jaridar Legit.ng ta rahoto.
Matashin ya gayawa majiyar mu cewa, bayan samun nasarar zuwa jami’ar Windsor wacce ke a birnin Ontario na ƙasar Canada, an kuma zaɓe shi a matsayin wakilin ɗalibai wanda wanann babban matsayi ne a jami’ar.