- Wani magidanci mai suna Abiodun Akinyemi ya bukaci wata kotun Kwastamari data raba aurensa da matarsa Christina.
- Akinyemi yace matarsa ta tilasta shi fakewa a coci a lokacin da ya kasa jure wahalhalun data jefa ciki.
- Ya mai Shari’a, banji dadin rayuwa ta ba cikin shekaru 18 da suka wuce tun da muka yi aure da Christiana.
Wani magidanci mai suna Abiodun Akinyemi ya shaida wa wata kotun Kwastamari ta Mapo Grade’A’ da ke Ibadan cewa ta raba aurensa da matarsa Christina mai shekaru 18 da haihuwa, saboda tana jefa rayuwarsa cikin kunci,Vanguard ta rawaito.
Da yake ba da shaida a gaban kotun, Akinyemi da ke zaune a Olodo ya shaida wa kotun cewa, “An tilasta ni na fake a coci a lokacin da na kasa jure wahalhalun data jefa ni ciki.
KARANTA WANNAN LABARIN: Dan wasan Bayan Barcelona Zai Bar Kungiyar
“Ya mai Shari’a, rayuwa ba ta yi mini sauƙi ba a cikin shekaru 18 da suka wuce tun da muka yi aure da Christiana.
“Hasali ma, tana zuwa wurin aiki na a kai a kai don ta tayar da hargitsi da kuma tsangwama.
“Don guje wa zubar da jini, na bar gida na ci gaba da zama a coci amma Christiana ba ta daina zuwa don ta dame ni da kuma yin fada da ni ba.
“Mafi muni kuma, Christiana tana yin duk wani yunƙuri na kashe ni kuma ba na sha’awarta.
“Don Allah a ba ni rikon ‘ya’yana hudu, ka umarce ta ta fita daga gidana,” Akinyemi ya roki kotu.
Sai dai kuma a cikin tagaddamar, Christiana ta ce mijin nata bai da alhaki matuka.
Wanda ake kara, wadda mai kula da abinci ce ta ce: “Mijina ya gaya mani cewa limamin cocinsa ya sanar da shi cewa ni ce sanadin sanya shi cikin wahala da matsalolinsa.
“Bayan haka, bai biya kudin makarantar yaranmu ba. Bugu da ƙari, na je ofishin Akinyemi saboda ya daɗe bai zo gare ni ba kuma yara suna buƙatar wani abu.”
Bayan sauraron shaidar ma’auratan, shugabar kotun, Mrs S.M. Akintayo ta shawarci mai kara da wanda ake kara da su wanzar da zaman lafiya da kwanciyar hankali yayin da ta dage karar har zuwa 3 ga watan Agusta domin yanke hukunci.
A wani labarin kuma, Shugaba Buhari Ya Rantsar Da Kwamishinonin RMAFC Guda Bakwai
Shugaban kasa, Muhammad Buhari, ya rantsar da kwamishinonin gwamnatin tarayya guda bakwai.
An gudanar da bikin ne a gaban taron majalisar zartarwa ta tarayya a fadar gwamnati da ke Abuja.
Mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ya mika rahoton kwamitin kawo sauyi kan harkokin lafiya ga shugaba Buhari.