Matatar Mai Dake Edo Zai Fara Aiki Nan da Karshe Watan Agusta
Gwamanan Edo Godwin Obaseki ya bayyana cewar Matatar Mai dake Edo zai fara aiki nan da karshen watan Agusta na wannan shekarar.
Gwamana Obaseki ya bayyana hakane ne lokacin da yakai ziyara a matatar Mai dake Karamar Hukumar Ologbo, Ikpoba Okha dake jihar Edo wanda AIPCC ta gina.
KARANTA:-Matar Gwamanan Sokoto Mairo Tambuwal ta Bukaci Yan Najeriya Dasu Dukufa Dayin Addu’a
A lokacin da yake zantawa da manema labarai yace aikin yayi matukar sauri duk da matsalar cutar Covid-19 data garwaye duniya.
Ya bayyana cewa hukumar dake kuka da ayyukan sun gwada don ganin yiwuwar fara aikin sun tabbatar babu matsala.
Yace hakan zai kawo Karshen sayar da danyan maj wanda akeyi nan da sati biyu masu zuwa.
Yace duk da tsaiko da aka samu na cutar Covid-19 matatar man zata iya karbar danyan Mai kuma tayi aikinshi yadda ya kamata.
Yace ina fata nan da karshen watan Agusta aikin zai kan kankama.
Mr. Tim Tian mai kula da hakkokin kamfanin ya yaba da ayyukan da sukeyi yace nan da bada jimawa ba aiki zai kankama.
Yace kamfanin shirye yake da ya fara karbar danyan Mai don sarrafashi zuwa sauran kayayyaki daban-daban.