Shugaban rukunin kamfanin Dangote wato Aliko Dangote ya bayyana cewa sabuwar matatar Mansa mai tace Lita 650,000kowace rana, za ta dauki matasan Najeriya 100,000 aikin yi da kuma samar da sama da dala biliyan 21, don ceton wa kasar nan makudan kudaden da za a yi amfani da su wajen shigo da mai. Kamar yadda Independent Post ta ruwaito.
A cewar hamshakin dan kasuwar, kamfanin yanzu yana da ma’aikata sama da 33,000.
KARANTA WANNAN LABARIN: Bankuna Yanzu Zasu Iya Bayar Da Katin Ƙasa — FG
Sai dai kuma abin da ya faranta wa ‘yan Najeriya rai shi ne, Dangote ya ce kaddamar da sabon Matatar Man, na dogaro da kai ne domin tace man fetur da fitar da shi kamar yadda aka samu cigaba a bangaren Siminti da takin zamani.
Dangote ya koka da cewa matsalar man fetur da ake fama da ita a halin yanzu tana da mummunan tasiri ga tattalin arzikin kasar nan kuma hakan ne ma yasa ya dauki matakin gina matatar mai da za ta sauya yanayin.
Idan ba amanta ba, Shugaban kasa Muhammadu Buhari, da takwarorinsa na kasashen Afrika biyar na daga cikin wadanda suka halarci taron kaddamar da matatar Man da ya gudana ranar Litinin a jihar Legas.
A wani labarin kuma, Dalilin Da Yasa Buhari Ya Amince Da Cire Wasu Kudaden Kwanaki Kadan Kafin Saukarsa A Mulki – FG
A ranar Laraba Fadar shugaban kasa, ta bayyana cewa, Shugaba Muhamamdu Buhari ya ba da umarnin cire wasu kudade kwanaki kalilan kafin mika mulki ga shugaba mai jiran Gado Bola Tinubu, saboda gwamnatin na bukatar kudi domin biyan wasu basussuka. Kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Mataimaki na mussamman ga shugaban kan Kafafen yaɗa labarai, Femi Adesina ne ya bayyana hakan yayin da yake jawabi a cikin shirin siyasa na gidan Telebijin na Channels mai suna Politics Today” yayin da ake karin haske akan ayyukan da gwamnatin shugaba Buhari ta aiwatar a cikin shekaru 8.