Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya amince da sake nada manyan masu bashi shawara 8, wadanda ya kora daga aikin su a mako daya gabata.
Sakataran harkokin yau da kullun na gwamnatin jihar Yakubu Haidara, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.
Wadanda aka sake nadawan akwai Aminu Abdullahi-Alkali Mai bada shawara a kan cigaban kudurorin, Ahmed Muktar Mohammed Mai bada shawara akan tsare-tsaren Burane, da kuma Junaidu Aminu-Kaura Mai bada shawara a kan harkokin shari’a
Sauran sun hadar da: Ibrahim Ma’aji-Gusau Mai bada shawara a kan hakkokin siyasa, Dakta Aslam Aliyu Mai bada shawara a kan Koyan Sana’o’i, Yusuf Abubakar-Zugu, Danyaro Abdullahi-Wuya, da Abubakar Musa Mainera.
KARANTA WANNAN LABARIN: Jirgin Saman Rasha ya yi Batan Dabo
Haidara ya kuma ce, wannan sabon nadin, zai fara aiki ne a nan take .
Idan za’a iya tunawa dai a ranar 3 gawatan Yuli shekaran na nan ne, Gwamna Matawalle ya kori dukkannin manyan masu bashi shawara.
Sai dai a karshe Gwamnan jihar Zamfara bai bada hujja kan daukan wannan matakin ba.
Comments 1