Matawalle ya umarci Mazauna Zamfara dasu ɗauki Makamai su kare kansu akan ƴan bindiga
Gwamnatin Jahar Zamfara ta buƙaci mutanen jahar dasu ɗauki makamai su kare kan su akan ƴan bindiga.
Da yake kokawa akan yawaitar hare-hare a Jahar, Hukumomin Jahar Zamfara sun umarci Kwamishinan Ƴan Sanda daya bada lasisin rike bindiga ga wanda suka isa riƙe bindiga a Jahar.
KARANTA WANNAN LABARIN: Mutane 6 Sun Mutu, 4 Sun Sami Rauni A Hadarin Mota A Jihar Jigawa–FRSC
Gwamnatin tace a shirye take ta taimakawa ƴan Jahar su riƙe makamai musamman Manoma, domin su kare kan su.
“Biyo bayan yawaitar aikace-aikacen ƴan bindiga a Jahar a sassa da dama na Jahar, da kuma ƙudirin Gwamnati na Tabbatar Da tsaron rayuka da Dukiyoyin Al’ummar Jahar, musamman a lokacin Damina, Gwamnatin ta yanke hukunci akan ɗaukar matakai akan yawaitar hare-haren ƴan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma sanya Jangali ga Al’umma.”
“Ta’addancin nan ya zama abin damuwa ga Al’umma da Gwamnatin Jaha. A saboda haka, domin ɗaukar matakai yanda suka kamata, ba tada wani zaɓi, in ba ta sanya wannan Dokokin ba.
“Gwamnati ta umarci mutane su mallaki makamai, ta baiwa Kwamishinan Ƴan Sanda umarni ya bada lasisin rike bindiga a garesu. A shirye Gwamnati take ta taimakawa Manoma su samo bindigu, sannan Gwamnati zata raba takardu a faɗin masarautu 19 na Jihar ga wanda suke Son su mallaki makamai don kare kan su.