Matsafa sun hallaka wata Ƙaramar Yarinya a Jihar Filato
An tsinci gawar Maryam Salisu mai shekara 14 a unguwar Babale dake karamar hukumar Jos ta Arewa a jihar Filato.
KARANTA WANNAN LABARIN: Yanzu-Yanzu: Wani Tsohon Dan Majalissar Wakilai Ya Rasu
Wata majiya ta shaidawa DAILY POST cewa an tsinci gawar yarinyar a cikin ramin tare da cire mata idanu, nono, hakori da harshenta.
Majiyar ta ce an kai wa Maryam hari ne a lokacin da take diban itace a wani daji da ke kusa da unguwar.
Majiyar ta bayyana cewa, Fatima Danliti, mahaifiyar marigayiyar, ta yi kuka a fili yayin da take ba da labarin haduwarta da diyarta ta karshe, inda ta ce ta barwa Allah komai.
Mahaifiyar ta lura, “Abin da ke da zafi amma ba abin da zan iya yi. An bar wa wanda ya aikata laifin da Allah”.
Daya daga cikin ‘yan matan Aisha Sani da ta shaida lamarin ta ce suna tare ne sai mutumin ya bugi Maryam a kai.
Majiyar ta bayyana cewa marigayin tare da wasu ‘yan mata 12, sun je wani daji da ke kusa da su nemo itace a lokacin da aka kai wa Fatima hari, yayin da sauran su suka gudu domin tsira da rayukansu.
A wani labarin kuma: Yanzu an wuce Zamanin magudin zabe – INEC
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, ta yi alkawarin tabbatar da kare kuri’un da ƴan Najeriya suka kaɗa a zaɓukan da ke tafe, inda ta ce zamanin magudin zaɓe ya wuce.
Shugaban Hukumar ta INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, ya yi wannan alkawarin ne a ranar Juma’a a lokacin da yake gabatar da jawabi a taron kaddamar da rahoton Yiaga Africa Election Analysis Dashboard, ERAD akan tura sakamakon zaɓe ta yanar gizo, a zaben Ekiti da Osun na 2022 a Abuja.