Kamfanin Man Fetur na kasa ya ce dogayen layukan da ake samu a gidajen Mai, ya kusa zama tarihi sakamakon odar Man sama da Lita Biliyan 2.1.
Bayanin hakan na kunshe cikin wata sanarwa da Kamfanin ya fitar, Mai dauke da sa hannun Shugaban sashin Hulda da jamaa na Kamfanin, tare da rabata ga manema labarai.
Sanarwa ta ce Shugaban Kamfanin Mele Kyari ne ya tabbatar da hakan, lokacin da ya bayyana gaban Kwamitin Majalisar wakilai mai kula da harkokin man Fetur.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a baya, Kamfanin NNPC ya ce samun Dogayen Layukan na da alaka da shigo da gurbataccen Mai da wasu Yan Kasuwar dakon man suka Yi.