Matar shugaban kasar ta ce idan har ana so a kawo karshen matsalar rashin tsaro a Nijeriya, to dole ne a cire bambanci tsakanin mace da namiji a gidan soja. Inda ta ce suma mata sojoji a bar su su gwada kwanjinsu.
Aisha Buhari ta dora alhakin rashin samun nasara da ake akan ‘yan ta’addan kasar nan da hana sojoji mata su fita su gwada bajintarsu a filin daga.
A ranar Alhamis ne 12 ga watan Satumbar nan matar shugaban kasar Najeriya Aisha Buhari, tayi kira ga hukumomin tsaro na kasar nan da su tura sojoji mata suyi yaki da matsalar tsaro a wasu jihohi na kasar nan. Da take magana a wajen wani taro da hukumar tsaro take gabatarwa a kowacce shekara a Abuja, matar shugaban kasar ta dora alhakin matsalar tsaron da ake samu da rashin bawa sojoji mata su gwada bajintarsu a fannin tsaro.
Aisha Buhari wacce ta samu wakilcin mai taimaka mata ta musamman Dr. Hajo Sani, ta bayyana cewa idan har ana son samun cigaba a bangaren tsaro a Najeriya to dole ne a cire wariya tsakanin mace da namiji. Haka shima da yake magana a wajen taron, shugaban ma’aikatan hukumar tsaro ta kasa Janar Gabriel Olonisakin ya ce hukumar soji ta sanya kashi 27.7 cikin 100 a fannin kawo zaman lafiya a Najeriya