Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi kira ga jama’ar jihar Katsina da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga da su kara hakuri a daidai lokacin da ya ce jami’an tsaro na kara daukar matakan shawo kan matsalar da gaggawa.
Shugaban kasar ya bayyana hakan ne a cikin sanarwar da Kakakin fadar shugaban kaasa, Garba Shehu ya fitar.
Sha’anin kalubalen tsaro na kara ta’azzara a jihar ta Katsina, inda a kullum ake samun rahotannin kisan jama’a ko sace su domin karbar kudin fansa, fyade da kuma sace dukiyoyin al’umma, lamarin da ya janyo zanga-zanga a wasu yankunan jihar.
Sai dai sanarwar ta yi gargadin cewa yin zanga-zangar zai iya kawo cikas ga kokarin da sojojin kasar suke yi na yaki da ta’addanci a jihar.