Sheikh Muhammad Kabir Qassim, mataimakin Limamin Masallacin Jema’a dake Kafanchan a jihar Kaduna ya shawarci Musulmi da su gudanar da azumi gwargwadon koyarwar addininsu domin yin addu’o’in zaman lafiya ga kasa.
Daruruwan Musulmi ne dai mabiya Darikar Tijjaniya a ranar Asabar suka taru a Jema’a a babban Masallacin Juma’a na Kafanchan dake jihar Kaduna domin gudanar da addu’o’in shekara-shekara da zikiri da addu’o’i na musamman domin yadda aka shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1441.
Sun gudanar da wannan taron addu’o’in ne a karkashin kungiyar Ansaru Faidhatu Tijjaniyya, inda al’ummar Musulmi na ciki da wajen masarautar Jema’a suka taru a Da’ira suka gudanar da addu’o’in.
Manyan membobin kungiyar ne suka jagoranci jawabin a wurin taron, inda suka yi jawaban hadin kai da kuma addu’o’in zaman lafiya ga kasa.
Haka zalika, Alhaji Husain Muhammad-Tahir, shugaban Ansaru Faidhatu Tijjaniyya, a Kafanchan, ya yi kira ga Iyaye da su koyar da ‘ya’yansu kyawawan dabi’u.