Babban Mai rikon Mukamin Sufetan Janar na Yan Sandar Najeriya Mista Usman Baba ya ce matsalar tsaron Najeriya ba fa wai ta fi karfin su ba ne, kuma za su iya kawar da ita.
Cikin wata sanarwa mai dauke da sanya hannun Kakakin Rundunar Frank Mba, ya umarci mataimakan sufeta janar na yan sanda, da Kwamishinonin yan sanda gamida manyan kwamandojin tsaro, da su tashi tsaye haikan wajen yaki da harka tsaron na.
Da ma dai tuni Mai rikon Mukamin Sufetan ya bada umarnin jibge jami’an tsaro a fadin kasar nan don kula da yanayin tsaro a bukukuwan Sallah.
Ya ce an dauki matakin jibge jami’an tsaron ne don tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin al’umma, a yayin bukukuwan Sallar, musamman yadda alumara suke kara rinchaɓewa.
Ya kuma tabbatar wa yan Najeriya cewa rundunar yan sandar karkashin kulawarsa, tana wasu shirye-shirye na sirri da za a ga bayan yan ta’adda a kasarnan.
Daga bisani ya kuma bukaci Jama’a da su ma su tashi tsaye wajen kai rahoton duk lamari da basu gamsu da shi ba izuwa hukumomin Tsaro.