Kwanaki uku bayan kashe sama da mutane 81 a jihar Borno, Boko Haram sun sake kai wa Jami’an soji hari tare sa bude musu wuta a yayin da suke bakin aiki.
A ranar Talata ne ‘Yan tada kayar bayan suka kai hari kauyen Zowo dake jihar ta Borno inda suka kashe mutane kimamin 81, tare kashe dabobbi guda 23; wanda ya hada Shanu, Akuyoyi, Jakuna da sauransu, daga bisani kuma suka garkuwa da mata da dama.
A jiya shugaba Muhammadu Buhari ya sake kira tare da bawa Jami’an sojin kasar nan Kwarin guiwa da su zage damtse wajen ci gaba da samun nasara akan ‘yan tada kayar bayan.
https://dimokuradiyya.com.ng/yan-boko-haram-sun-kashe-sojoji-shida-bayan-kai-musu-hari-a-borno/
Amma duk da wannan kira na shugaban kasa, ‘yan tada kayar bayan basu saduda ba, inda suka kai wa sojoji hari da suke bakin aiki a Monguno.
Daya daga cikin jami’an sojin da suke bakin aiki ya bayyanawa jaridar ‘TheCable’ cewa ‘yan tada kayar bayan sun far musu ne a yayin da suke tsakiyar aiki.
‘Yan tada kayar bayan sun biyo barauniyar hanya ne tare da far wa sojojin ba tare da sun ankara da su ba, kuma sun ci karfinsu saboda basu san da zuwansu ba.