Gwamnatin tarayyar Nijeriya ta yi kira ga manyan kasashen duniya da su sakar wa Nijeriya mara domin sayarwa da Nijeriya Makamai da dangogin kayayyakin yaki domin yaki da ‘yan ta’adda da suka addabi kasar.
Ministan yada labarai da al’adu na Nijeriya, Lai Mohammed ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Nijeriya, inda ya jaddada bukatar da yake akwai ga manyan kasashen na duniya da su daina kafa hujjoji ta batutuwa da ba su taka kara sun karya ba wajen hanawa Nijeriya cinikin makamai.