Abubakar Sani Bello Lolo gwamnan Jahar Neja yayi kira ga jami’an Fikira na Najeriya, da su bullo da dabarori da salo don cigaba da zakulo Yan ta’adda da bata gari da kuma dakile miyagun ayyuka a kasar nan.
Gwamnan yana magana ne kan jami’an fikira na Shinkafi wanda take karkashin jagorancin Umar Shinkafi, da aka gabatar a Abuja a jiya Laraba. Kamar yadda Jaridar Tvcnews ta wallafa a shafinta
Wanda jami’an sun maida hankali kan garkuwa da mutane da kuma ta’addanci dake faruwa a Najeriya.
KARANTA:- WASANNI: Marcus Rashford zai yi jinyar wata uku sakamakon tiyata da za’ayi masa a kafada
Gwamna Abubakar Sani Bello Lolo ya nuna alhininnsa kan yadda ta’addanci da garkuwa da mutane yayi kamari a Jahar sa, wanda yayi bayanin yadda gwamnatin sa take iya bakin kokarinta wajan dakile ta’addanci amman abun yaci tura, inda Yan ta’addan ba sa da alamar sassautawa.
Gwamnan yace yana daga cikin yunkurin sa da dakile ta’addanci na rashin biyan kudin fansa, inda gwamnan yace wannan yana taimakawa Yan ta’addan wajan sayen makamai.
Gwamnan yace da zarar mun tura jami’an tsaro nan da nan sai Yan ta’addan su sauya wajan zama saboda samun rahotan da sukeyi daga bata gari.
A lokacin da yake magana kan batun samar da Yan sanda Jaha, cewa yayi abune mai amfani duba da mutanen Najeriya karuwa sukeyi koda yaushe, a yanayin da muke ciki ba za muki samar da Yan sandan Jaha ba, saboda yawan Yan Najeriya ya tasamma miliyan dari biyu.
Ya kuma yaba da irin kokarin da Shuwagabannin addinai da Sarakunan gargajiya kan irin kokarin su na kawo karshen ta’addanci a kasar nan
A yayin da yake kara jinjinawa kungiyar jami’an fikira na Shinkafi karkashin jagorancin Alhaji Umar Aliyu Shinkafi, gwamna Abubakar Sani Bello Lolo yace jami’ai ne na musamman, wanda himmar su da kokarin su ya karade garuruwan mu.
Gwamnan ya bada shawarar hada kai da kungiyoyin Yan Sakai wajan yaki da ta’addanci, yace yanada kyau a janyo mutane masu dabi’u mai kyau a harkar.