Gwamnan jihar Abia Dakta Okezie Ikpeazu ya kaddamar da wata tawaga, karkashin jagorancin Mai taimmakami shi kan kula da harkokin Dalibai na jihar Mr Chibuzo Ndom, domin zuwa jami’ar Jos dake jihar Fulato, don kwaso dukkannin dalibai yan asalin jihar ta Abia, wadanda su ke zaune cikin fargaba, sakamakon tashin hankalin da ka samu, wanda ya yi sanadiyar garkame jami’ar.
Hakan na zuwa ne bayan wani koke da daliban jami’ar Jos din suka shigar a ranar Alhamis din data gabata, kan cewa, wasu bata gari, ma kai musu hari, Wanda hakan ya yi sanadiyar kashe dalibai 4 cikin kwanaki biyar da suka gabata.
KARANTA WANNAN LABARIN: Hukumar EFCC ta rabu da kaddarar Kwankwaso da ta garkame
A cewar Kwamishinan yada labarai na jihar Abia John Okiyi Kalu, tawagar da aka tura, sun hada da Jami’an tsaro, domin tabbatar da cewa, daliban jihar sama da 200 dake karatu a jami’ar, sun dawo Umuahia babban birnin jihar lami lafiya, Wanda kuma gwamnan jihar ne zai tarbesu ya yin isowar su gida.
Awani labarin Kuma na daban.
Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje ya ce, kirkirar Karin Masarautu guda 4 a Jihar, ya nuna irin yadda suka jajirce a kudirin su na inganta Masarautun Gargajiya a Jihar.
Ya bayyana haka a lokacin bikin Mika sandar Mulki na Mai Martaba Sarkin Bichi Nasiru Ado Bayero, a Filin Kwallo na Bichi a ranar Asabar, inda ya bada tabbacin cewa, zai ci gaba da yin iya kokarin shi, na bada dukkanin goyon baya ga masu ruke da Sarautun Gargajiya a Jihar Kano.
Wannan na Kunshe ne a cikin wata sanarwa da Sakataren Yan Jarida na Gwamnan Abba Anwar, ya fitar a ranar jiya Asabar, 21 ga watan Ogustan Shekarar 2021.
Inda sanarwar ta ce, “Kirkirar Karin Masarautu guda 4, Wanda Masarautar Bichi ke ciki, ya nuna a fili yadda muke son inganta Masarautun Gargajiya a Jihar Kano, Wanda da Wannan ci gaba zaije har Kasa,” inji shi.
Dayake bayyana godiyar sa ga wadanda suka halarci taron, Gwamnan ya yaba da yadda suka nuna abokantaka da Kuma amsar goron gayyata.
“Ina farin ciki na yadda nake a wannan taro na mika sandar Mulki ga wani Sarki Mai Daraja ta daya na Masarautar Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero. Sarki na biyu a Masarautar Bichi. Ya kasan ce ‘Da ne ga Sarkin Fulani na 13 na Kano, Marigayi Alhaji Ado Bayero” inji Ganduje.
Dayake bayyana irin yadda Sarkin Bichi yake, Gwamna Ganduje ya ce ” Sarkin Bichi ya Kasan ce Mai son Al’umma, Wanda yayi aikin Banki, kuma Dan Kasuwa ne daya samu nasarori a rayuwa.”a. cewar Gwamna Ganduje.
Kazalika Gwamna Ganduje ya tunatar da cewa, kafin nada Sarkin Bichi, ya kasan ce Hakimin Nasarawa, Kuma Shugaban Karamar Hukumar Tarauni, inda ya kara da cewa, ya kuma rike mukamin Turaki da Chiroman Kano. Don haka zabar shi a matsayin Sarkin Bichi abune daya cancanta.
Ya bayyana fatan cewa, Masarautar Bichi zata samu gyare-gyare da dama Karkashin jagorancin Alhaji Nasiru Ado Bayero.
Gwamna Abdullahi Ganduje ya kuma yaba da irin gudunmuwar da masu rike da Sarautun Gargajiya suke bayar wa, wajen bunkasa zaman lafiya da zumunci a tsakanin Al’ummar Jihar Kano.
A nashi jawabin, Wakilin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, wanda kuma shi ne Shugaban Ma’aikatan Shugaban Kasa Farfesa Ibrahim Gambari, ya sanar da godiyar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga Sarkin Bichi.
A cewar sa, Shugaban Kasa ya taya Mai Martaba Sarkin Bichi murna akan cancantar da ya yi, na nadashi a matsayin Sarkin Bichi.
Kazalika ya ce, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari “Abokina Marigayi Mai Martaba Sarkin Kano Alhaji Ado Bayero ya kasan ce mai inganta hadin kai, bawai a Masarautar shi ba, har ma a Nigeria baki daya.
A jawabin shi, Mai Martaba Sarkin Bichi Alhaji Nasiru Ado Bayero ya godema Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Gwamna Ganduje da irin goyon bayan da suke bashi.
Ya kuma yi Kira ga Al’umma dasu rika dasa itatuwa, domin samar da yanayi Mai tsafta, Yana mai bada tabbacin samar da tsaro a cikin Al’umma.
Comments 1