Biyo bayan harin da yan bindiga su ka kai a Makarantar Bethel Baptist a yau Litinin, Gwamnatin jihar Kaduna ta bada umarnin rufe makarantu goma sha uku, a wasu yankuna da ake tsammanin yan bindiga zasu iya kai hare-hare.
Haryanzu dai ba’a fayyace adadin daliban da aka sace a Makarantar da ke karamar hukumar Chikun na jihar Kaduna ba.
Umarnin rufe makarantun ya zo ne cikin wata sanarwa da Babban Daraktar hukumar kula da ingancin ilimi na ma’aikatar Ilimi ta jihar Umma Ahmed ta fitar a yau, kuma ta raba wa makarantu masu zaman kansu, inda ta ce, umarnin zai fara aiki ne a nan take.
Kana sanarwar ta yi kargadi kan kin yin biyayya ga wannan doka da gwamnatin jihar ta saka.
KARANTA WANNAN SANARWAR: Mata sun tare hanyar Kachia bayan sace dalibai
Kazalika ta bayyana sunayen makarantun da wannan doka ta shafa kamar haka: Faith Academy dake kan hanyar Kachia kusa da Jakaranda, Deeper Life Academy dake Maraban Rido, Ecwa Secondary School dake Unguwar Maje, Bethel Baptist High School dake Damishi.
Sauran sun hada da: St. Peters Minor Seminary dake Katari, Prelude Secondary School dake Kujama, Ibiso Secondary School dake Tashar Iche, Dukkannin makarantun “Tulip International” biyu na (Maza da na Miata).
Ragowar makarantun sun hada da Goodnews Secondary School da St. Augustine da suke Kujama, Comprehensive Development Institution (CDI) dake Tudun Mare, da kuma Adventist College dake Kujama.