Matsalar Tsaro: Idan da ba Buhari ke Mulki ba, da tuni Matsalolin Tsaro tafi haka lalacewa a Najeriya — Ayade
Gwamnan Jahar Cross River Ben Ayade yace idan da badan ƙoƙarin da Buhari keyi ba, da tuni Matsalar Tsaron Najeriya tafi yanda take a yanzu.
KARANTA WANNAN LABARIN: 2023: Bazan taɓa ajiye Ƙudirin Tsayawa takarar Shugaban Ƙasa ba — Kalu
Ayade wanda ya bayyana haka a lokacin da yake jawabi ga Manema labaru bayan taro da Shugaban Ƙasa a Fadarsa dake Villa, Abuja a ranar Talata, ya yabawa Shugaban Ƙasar akan fahimtar sa akan matsalolin tsaro na Ƙasa dama na Ƙasashen waje, yana mai bayyana cewar ya samu nasara wajen daƙile Ƴan bindiga da ƴan Boko Haram.
Ayade yace “bari in fara yabawa akan Ilmin Buhari, da fahimtar sa akan matsalolin tsaro na gida dana waje, da kuma abinda yayi domin samun nasarar daƙile ƴan bindiga da ƴan Boko Haram a Najeriya.
Ya cigaba dacewa”wannan ƙasar da zama cikin mawuyacin hali, amma Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya hana ta zama irin Ƙasar Afghanistan, idan akayi la’akari da irin ƙungiyoyin dake yawan ɓullo wa wanda suke da ƙudirin cewa yankin Afirka ta Yamma nasu ne, saboda haka Musulmi da Kiristoci dake yankin dole a ƙarar dasu.