Matsalar Tsaro: Kayi Koyi da Boris Johnson ka sauka daga Mulki — Ƴan Najeriya ga Buhari
Biyo bayan yawaitar Matsalar Tsaro a Ƙasar, wasu masu ruwa da tsaki sun jaddada cewa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka a matsayin Shugaban Nijeriya.
Majiyar Jaridar Dimokuraɗiyya ta ruwaito cewa ƴan Ta’adda sun kasance suna cigaba da gudanar da ta’addanci a Ƙasar, suna Cigaba da kawo rashin zaman lafiya ga Al’umma.
KARANTA WANNAN LABARIN: Kotu ta Kori Ɗan Takarar Gwamnan PDP a Delta
Matsalar tsaro dake cigaba da fuskantar Ƙasar a ranar Talata 5 ga watan yunin, ƴan ta’adda sun kai hari ga Manyan Gwamnati, ciki har da waɗanda ke aiki da Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari.
Ayarin Shugaban Ƙasa an kai masu hari a Katsina a ranar Talata. A cewar rahoto, guda biyu daga cikin Jami’an su an jikkata su.
Sakamakon hare-hare da Kashe-kashe da ke cigaba da wakana a Ƙasa, ya fusata wasu masu amfani da Kafafen Sadarwa na Zamani suka yi kiran a daina wani gangamin yaƙin neman zaɓe, da sauran aikace-aikacen da suka shafi Babban Zaɓen mai zuwa.
Sun bayyana fatan cewa zaɓen bazai faru ba, suna masu bada misali ga aikace-aikacen ta’addanci dake wakana a faɗin ƙasar.
Da yake jawabi, Shugaban Ƙungiyar Marubuta Kare Haƙƙin Bil’adama HURIWA Emmanuel Onwubiko yace Zaɓe dole a yi shi idan Shugaban Ƙasa yaki sauka daga Mulki.
A cewar sa “Buhari baya buƙatar a gaya mashi ya ajiye aiki, idan shi ya cancanta. Babban abinda ya kamata mutum yayi ya sauka, kuma bashi da wani magani ga kowacce matsaloli tun daga farkon Gwamnatin sa.
Haka zalika, wani Jigo a Jam’iyyar PDP wanda yayi jawabi daga Jahar Benue daya bukaci a sakaye sunan sa, ya yi kira ga Shugaban Ƙasa daya amshi kiran ƴan Najeriya ya sauka daga mulki, kamar yadda Firaministan Landan Boris Johnson ya yi.
Yace “Shuwagabannin Afirka a kowane lokaci so suke su mutu suna kan mulki. Ƴan Najeriya sun daɗe suna kira ga Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya sauka, amma har yanzu yana nan a Villa, shin wannan shine Shugaba.