Malaman addinin Islama na Madarasatul Nurul Islam, Quarters 123, Al-Nuriyyah Islamic Foundation da Al-Inara Islamic School Minna, sun gabatar da addu’o’i na musamman na neman Allah ya kawo mana dauki kan kalubalen tsaro da ke addabar jihar da Najeriya baki daya.
Babban mai kiran kuma jagoran Imani, Malam Muhammad Adam Bosso, ya ce an gudanar da taron addu’o’in ne bisa bin kiran da mai alfarma Sarkin Musulmi Alhaji Sa’ad Abubakar ya yi na a yi addu’o’i na musamman kan rashin tsaro da sauran kalubalen da kasar ke fuskanta.
Ya ce matsalar rashin tsaro da ake fama da ita a Najeriya na bukatar addu’o’i sosai, yana mai jaddada cewa akwai bukatar kowane dan kasa ya bayar da gudunmawa ta kowace hanya domin kawo karshen kashe-kashe da garkuwa da mutane da ake yi a kasar.
Mataimakin shugaban gidauniyar Al-Nuriyyah Islamic Foundation, Alhaji Usman Ayuba Katako, ya ce yara da dama sun zama marayu a Arewa sakamakon ayyukan ‘yan fashi da ayyukan Boko Haram.
Ya ce, “Addu’a ita ce Nijeriya ta samu zaman lafiya; addu’a ita ce shugabanni su ji tausayin jagora; su kuma mabiya su kasance da iyawa da jajircewa wajen yin mubaya’a ga shugabanni, ta yadda ‘yan fashi, Boko Haram, garkuwa da mutane da wadannan wahalhalu su zama tarihi.”