Kimanin Ƙungiyoyi 400 a Najeriya a ranar Alhamis suka yi kira ga Gwamnatin Tarayya data ƙara himma wajen yaƙi da matsalar tsaro dake yawaita a Ƙasar.
A cewar su, Matasan Najeriya bazasu cigaba da ganin wannan mummunan kisa da ake yi masu a kowace rana.
Ƙungiyoyin ƙarƙashin Ƙungiyar Ƙabilai ta Matasan Najeriya sun ce sun lura da yanayin tsaro a Ƙasar, wanda a halin yanzu yakai wani mataki na ban tsoro.
KARANTA WANNAN LABARIN: Shugaban Ƙasa Buhari Ya Sauka A Birnin Addis Ababa
Shugaban Ƙungiyar na NENYLC Terry Obirh ya bayyana haka a madadin Ƙungiyar a lokacin jawabin ta a Abuja, wanda Sakataren ta ya halarta Oladotun Hassan da kuma Sakataren Yaɗa Labaru Emmanuel Zopmal.
Yace “matsayar mu shin Gwamnatin Tarayya tana buƙatar ta zaman to mai maida hankali akan matsalar tsaro a Ƙasar, domin bazamu iya cigaba da kallo ana kashe ƴan Najeriya da yawansu a kullum.
“Babban mahimmancin Gwamnati shine kiyaye rayukan da dukiyoyin Al’umma amma wannan ba’a yinshi a Najeriya, Ana kashe ƴan Najeriya kamar kaji.
” A yau dai munce ya isa haka,muna kira ga hukumomin tsaro dasu tashi tsaye. Munji maganganu da dama daga Gwamnati, mun gaji da saƙon ta’aziyya, abinda muke so shine kawo ƙarshen kisa a Najeriya ko ta wace irin hanya.