Iba Gani Adams, Aare Ona Kakanfo na kasar Yarbawa, ya yi gargadin cewa Najeriya na iya kasa wanzuwa nan da shekaru biyu masu zuwa sakamakon yawaitar rikice-rikice a kasar.
Ya ci gaba da cewa aiwatar da gwamnatin tarayya cikin gaggawa na tsarin tarayya na gaskiya ita ce hanya daya tilo da za ta ceto al’ummar kasar daga fita daga kangin da take ciki.
Mulkin kasar ya nuna rashin hadin kai, a cewar basaraken na kabilar Yarbawa, inda ya kuma ce akwai matsalar rashin tsaro, tabarbarewar tattalin arziki, da tabarbarewar harkokin karatu da dai sauransu.
Shugaban jam’iyyar Odua People’s Congress, OPC, Adams, ya bayyana haka ne a wajen bikin Okota na bana a garin Arigidi-Akoko, na karamar hukumar Akoko ta Arewa-maso-Yamma a jihar Ondo.
A wani labarin kuma na daban.
Rahotannin da ke isowa daga garin Iseyin a jihar Oyo na nuni da cewa sarki Aseyin na Iseyin ya kwanta dama.
Sarkin wanda ya jima yana kwance a asibiti, rahotanni sun bayyana cewa ya rasu ne da safiyar ranar Lahadi a Asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan.
Gobe da safe za a dauke gawarsa daga asibiti zuwa garin kamar yadda majiyoyi a garin suka bayyana.
Wani tsohon dan majalisar dokokin jihar, dan asalin Iseyin, wanda ya zanta da Jaridar DAILY POST ya tabbatar da rasuwar sarkin.
Tsohon dan majalisar wanda ya nemi a sakaya sunansa ya ce, “Na kira wasu ne da na ji labarin da safe.”
“Daga baya sun tabbatar min da hakan da yammacin yau Lahadi”
“Aseyin ya mutu. Gobe da safe za a dauke gawarsa daga asibiti”.
Idan zaku tuna cewa sarakunan gargajiya akalla bakwai ne suka kwanta dama a cikin watanni tara da suka gabata a jihar Oyo.
Shahararren cikin sarakunan gargajiya shine Soun of Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi wanda ya rasu a ranar 12 ga watan Disambar shekrar 2021.
Oba Saliu Akanmu Adetunji, tsohon Olubadan ya rasu a ranar 2 ga watan Janairun wannan shekarar.
Alaafin 45 na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi shi ma ya rasu a watan Afrilun bana.