Hauhawar farashin kayan abinci da yanzu haka yake ci gaba da ta’azzara a mafi yawan sassan Najeriy, na ci gaba da ciwa yan kasar tuwo a kwarya.
Yayin da kuma a gefe guda yake kara rura wutar yunwa, sakamakon yadda manoma suka yi ta korafin cewa ‘yan ta’adda na karbe gonakinsu tare da hana su gudanar da ayyukansu na noma.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa a Arewacin kasar nan, inda akasarin noman kasuwanci ake yi idan aka yi la’akari da dimbin filayen noma, wasu manoman jihohin Zamfara, Katsina, Nasarawa da Binuwai, a wata tattaunawa da manema labarai sun koka da cewa rashin tsaro ya hana su cin gajiyar daminar bana.
2023: Mambobin Jam’iyyar PDP Sama 600 Ne Suka Sauya Sheka Zuwa APC A Jihar Gombe
Wasu daga cikinsu sun ce sai sun biya ‘yan ta’addan haraji domin samun damar shiga gonakinsu.
Ministan Noma da Raya Karkara, Mahmood Abubakar, ya jaddada hakan, a lokacin wani taron manema labarai na baya-bayan da manema labaran fadar shugaban kasa, inda ya ce hare-haren da ‘yan ta’adda ke kaiwa manoman sun hana manoma shiga gonakinsu.
Ya bayyana cewa lamarin da ya shafi wuraren sun haɗar da yankin Arewa maso Yamma da Arewa ta Tsakiya.
Sai dai ya ce gwamnati na kokarin shawo kan matsalar, cikin gaggawa don manoman su samu damar aiwatar da aikin su na noma.
Wani manomin shinkafa a jihar Zamfara, Alhaji Nuhu Deme, ya shaidawa Sunday PUNCH cewa farashin kayan abinci na iya ci gaba da hauhawa, kuma za a iya samun karancinsa matukar ba a yi wani abu ba don magance kalubalen.
Ya ce daman noman na bana zai kasance mafi kyau a cikin ‘yan shekarun nan idan aka yi la’akari da yanayin damina mai kyau amma ‘yan ta’adda sun ci gaba da kai farmaki, suna kashe su ko kuma sace manoman da suka su je gonakinsu.
Tabarbarewar tsaro ta kunno kai a jihar a lokacin da gwamna Bello Matawalle ya bayyana a watan Yuni cewa ya kamata jama’a su kare kansu da bindigogi, lamarin da ‘yan sanda da babban hafsan tsaron kasa, Janar Lucky Irabor suka yi watsi da batun.