
Matsalar tsaro ya kawo cikas ga karatun Mata a Arewa
Jaridar Thisday ta ruwaito Ahmad Lawan Shugaban Yan majalissu ya bayyana matsalar tsaro a Najeriya yana kawo dakushewar karatun Mata musamman Matan Arewa.
Yace ” shigar da Yan bindiga keyi makarantu suna kwashe Dalibai ya kawo babbar matsala tayadda Mata a Arewa suna gujema zuwa Makaranta.
KARANTA:- Wata kuto ta tura wasu mun uku gidan gyaran hali a Legas
Ahmad Lawan ya bayyana haka ne jiya Lahadi a Abuja inda aka gayyace shi a matsayin babban bako a wajen taron bikin Yaran Dammajalissa mai wakiltar Adamawa ta Yamma maso Gabas.
Ya cigaba da cewa ” wannan ba karamin mummunan cibaya bane ga harkar Ilimi inda har Yan bindiga sukan shiga Makarantu su kwashe Dalibai harda Mata.
Yace ” tun a baya harkar Ilimi a Arewa musamman Ilimin Mata na samun matsala kuma ga wannan rashin tsaro ya kara karfafa matsalar.
Yazama wajin mu damu zage damtse wajan yakar ta’addanci a Kasar mu mu dawo da zaman Lafiya domin cigan Al’ummar mu.
Sannan ya kara jawo hankalin matasa dasu rike al’adunsu wanda suka gada domin shine abun alfaharinmu kuma shine wayewa.
Yace yin aiki da abunda al’adarmu ta koya mana shine wayewa ba abunda mukaga wasu turowa sunayi ba.
Dan Jarida Binos yace ” Ahmad Lawan zaiyi kokarin ganin duk wata kabila an tabbatar da yin wani tsari na ajiye ka yayyakinsu na al’adu.