‘Yan bindiga sun kashe ‘yan banga tare da yin garkuwa da mutum 30 bayan sun shafe awanni suna suna tafka ta’asa a ƙaramar hukumar Nasarawa dake jihar Nasarawa.
Mazauna yankin sun ce maharan kimanin su 50 a kan babura sun tare hanyar Udege zuwa Loko na awanni inda suka kwashi mutanen a cikin daren Litinin.
Shugaban ƙaramar hukumar Muhammad Otto ya ce, ‘Yan bindigar sun kashe ‘yan banga guda biyu a kan Dutsen Onda, a kwaton-ɓaunar da suka yi wa ‘yan bangar da suka bi su domin ƙwato mutanen aka yi garkuwa da su”.
Sai dai a daidai lokacin da muke haɗa wannan rahoto bamu samu tattaunawa ASP Nansel Ramhan, wanda shi ne kakakin hukumar ‘yan sandan jihar ta Nassarawa.