Jaridar Katsina post ta rawaito cewa ‘yan bindiga sun kai farmaki a ƙananan hukumomin Batsari da Kurfi a daren ranar Talata duk da ƙarin jami’an tsaro da jihar ta samu daga gwamnatin tarayya.
Ƙauyukan da ‘yan bindigar suka kai hari sun haɗa da kauyen Karare dake Batsari, sai kuma kauyen Barkiya dake karamar hukumar Kurfi.
‘Yan bindigar sun kai mabanbanta farmakin ne tare da yin garkuwa da mai garin kauyen Karare, Ciroma Ahmadu Karare. Sun yi garkuwa da mata tare da dabobbi ds kuma kayan abinci.
Yayin da yake tattaunawa da manema labarai, wani mazaunin ƙauyen Karare mai suna Mustapha Ruma, ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun kawo farmakin ne ɗauke da muggan makamai.
Ruma ya kara da cewa sun yi garkuwa da wasu matan aure tare da yarinya mai gari ‘yar shekaru 20 a duniya.
Rahotonni sun gabata cewa akwai wata kata mai shekaru 23 a duniya tare da jaririnta dukkansu ‘yan bindigar sun yi garkuwa dasu.
Ruma ya ƙara da cewa, wannan lamari ya sanya mutane da dama ƙauyen kaura daga ƙauyen zuwa wasu wuraren da suke ganin zasu samu zaman lafiya.