Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin Ilori Alhaji Usman Adamu, Harɗon Harɗoɗin Jihar Kwara.
Malam Ibrahim mazaunin garin Ilori, babban birnin Jihar Kwara ya shaida wa kamfanin dillancin labarai cewa ‘yan fashin sun yi garkuwa da Sarkin Fulanin da safiyar Alhamis 3 ga watan Satumba a cikin garin Ilori.
“Yana cikin mota ne tare da ɗansa mai suna Babangida kuma ana zaton yana kan hanyarsa ce ta zuwa banki, yana ɗauke da kuɗi da zai kai banki.
“Mutanen sun tare masa hanya ne da motarsu, suka sa shi ya fito sai suka tafi da shi a cikin motarsu.
http://dimokuradiyya.com.ng/yan-bindiga-sun-yi-garkuwa-da-mutane-20-a-jihar-neja/
“Lamarin ya faru ne a cikin garin Ilori, a safiyar ranar Alhamis, a daidai kofar Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ilori.
“Daga baya an gano motarsa da wayoyinsa a cikin motar, yanzu haka motar na ofishin hukumar ‘yan sandan jihar Kwara”, kamar yadda ya bayyana.
Uwargidan Sarkin Fulanin, Hajiya Aina’u, ta tabbatar wa manema labarai cewa an yi garkuwa da mijin nata, inda ta buƙaci al’umma su sa shi a addu’ar kuɓuta daga hannun ‘yan bindigar.