Kungiyar harkokin addinin Muslunci ƙarƙashin jagoranci Sarkin Musulmi Muhammad Sa’ad Abubakar na III, ta ja hankalin gwamnatin tarayya da cewa ‘yan Najeriya na da damar fadar albarkacin bakinsu a duk lokacin da suka ga wani abu yana tafiya ba daidai ba, musamman a wannan lokaci da arewacin ƙasar nan ya tsinci kansa na rashin tsaro.
Ƙungiyar ta yi alawadai da irin yadda jami’an tsaron ƙasar nan ke ɗaukar matsalar da ta shafi garkuwa da mutane, kashe-kashe da sauran manyan laifuka a ƙasar nan ba a bakin komai ba.
Idan ba a manta ba a ‘yan kwanakin nan ne Farfesa Ango Abdullahi ƙarƙashin inuwar dattawan arewa, ya soki gwamnatin tarayya game da halin da arewacin ƙasar nan ke ciki.
Ƙungiyar ta kara da cewa abun takaici ne ace gwamnatin tarayya ta kasa yin komai game irin rashin tsaro da ake fuskanta, Boko Haram, ‘yan bindiga, garkuwa da mutane da uwa uba fyde duk sun addabi ƙasar nan.
Ƙungiyar tace da gwamnati tayi abinda ya dace da yanzu ba a shiga halin da aka tsinci kai a ciki ba.
Daga karshe kungiyar tace yana da gwamnati ta ɗauki dukkanin shawarwarin da ake bata ko da kuwa daga ɓangaren ‘yan adawa ne.