Tsohon Gwamnan Jahar Sokoto Attahiru Bafarawa yace Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari zai amsa tambayoyi daga Allah a dalilin Matsalolin tsaron dake fuskantar Ƙasar.
Bafarawa yace Buhari dole zai tunkari matsalolin tsaro a yankin Arewa maso Yamma da dukkanin ƙwazon shi, saboda zai amsa tambayoyi daga Allah.
Dayake jawabi ga Sashen Hausa na BBC, tsohon Gwamnan ya bayyana damuwar sa akan matsalolin tsaro a Sokoto da Jahar Zamfara.

KARANTA WANNAN LABARIN: Anfara Kada Kuri’a A Ihiala Dake Jihar Anambra
Yace “wannan Matsalar Tsaro annoba ce data ke damun mu. Yanayin Jahohin Sokoto da Zamfara, ƴan asalin garin kaɗai zasu iya bayyana abinda ke can.
“Abun baƙin ciki da muka sani shine tsaron ƙasar nan na hannun Gwamnatin Tarayya.
“Waɗanda ke gayawa Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari cewa komai lafiya ƙalau yake, ko kuma suna faɗa mashi cewa komau na tafiya lafiya ƙalau, to suna cutar damu, suna cutar dashi.