Gwamnan jihar Ribas, Nyesom Wike, ya ce gwamnatin APC ta ji kunya kan matsalar tsaron Nijeriya. Inda ya shawarci ‘yan’wansa gwamnoni na jam’iyyar APC da kada su ji kunyar amincewa da cewa jam’iyyarsu ta APC ta gaza wajen kare rayuka da dukiyoyin jama’ar Nijeriya.
Ya ce ba zai isa ba, idan gwamnonin suka amince da cewa akwai matsalar tsaro ba tare da sun ɗaura alhakin hakan a kan gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ba.
Bbc Hausa sun ce; yana magana ne yayin ƙaddamar da aikin wata hanya da gwamnan jihar Oyo ya samar a garin Obagi.
”Komai ya rushe a ƙasar nan, tsaro ya taɓarɓare, tattalin arziƙin ƙasa ya ruguje, ba wani abu dake tafiya a wannan ƙasar, yau matsalar tsaro ta shiga ko ina a Najeriya. APC ta ji kunya” inji gwamnan, kamar yadda jaridar The Punch ta rawaito.