Ministan watsa labarai da al’adu, Lai Mohammed, a ranar Litinin, ya tabbatarwa ‘yan Nigeria cewa gwamnatin tarayya ba ta da wani shiri na sanya sabuwar dokar kulle a Nigeria, yayin da kasar ke kokarin dakile yaduwar annobar Coronavirus karo na biyu.
Lai Mohammed, wanda ya zanta da manema labarai a Lagos, ya roki ‘yan Nigeria da su tabbatar sun kiyaye dukkanin dokokin kiyaye kai daga kamuwa da cutar da kwamitin PTF kan COVID-19 ya zayyana.
Ministan ya ce, “Dangane da batun kulle, bana tunanin akwai wani lokaci da gwamnati tace za ta sake kulle kasar karo na biyu. Sai dai, gwamnatin tarayya ba ta jin dadin yadda ‘yan Nigeria ke yin fatali da matakan kariya daga COVID-19 kamar sanya makarin fuska, ba da tazara, yawan wanke hannu, da kuma gujewa shiga tarukan jama’a.
“Idan har bamu kiyaye wadannan matakan ba, to annobar za ta ci gaba da mamaye ko ina kuma wannan sabuwar koronar tana da wuyar sha’ani, gwamnatin tarayya za ta ci gaba da nuna muhimmancin bin dokokin kare kai daga kamuwa da cutar karo na biyu.
“Gwamnatin tarayya na sane da matsin tattali da kuma kuncin rayuwa da dokar kulle karo na biyu ka iya jefa ‘yan Nigeria, don haka, ya zama wajibi yan kasar su tashi su kare kawunansu, ta hanyar bin dokoki da matakan kariyar na kamuwa da cutar.”
A watan Maris 2020 gwamnatin tarayya ta sanya dokar kulle a babban birnin tarayya Abuja, da jihohin Lagos da Ogun, na tsawon makwanni biyar. Daga bisani kuma sauran jihohi suka dauki irin wannan mataki domin dakile yaduwar cutar ta Corona.
Mutane da dama sun rasa ayyukansu, yayin da aka rufe tashoshin jiragen sama, bankuna, kamfanoni, da kuma sauran wuraren daukar mutane aiki, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.