A safiyar ranar juma’a ne haɗakar ƙungiyoyin kishin al’umma a garin Osogbo na jihar Osun suka fara gudanar da zanga-zangar lumana domin nuna adawarsu ga ƙarin farashin man fetur da kuma kuɗin wutar lantarki.
Rahotonni sun bayyana cewa, an fara gudanar da zanga-zangar ne da misalin ƙarfe 8:30 na safe a dandalin Freedom Park.
Masu zanga-zangar dai na ɗauke da kwalayen da ke ɗauke da kalaman nuna adawa da ƙarin kuɗin lantarki da kuma na man fetur wanda gwamnatin shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ta yi.
https://dimokuradiyya.com.ng/matsalar-tsaro-yadda-matasa-suka-yi-zanga-zanga-a-jihar-katsina/
Haka kuma masu zanga-zangar sun buƙaci gwamnatin da ta janye ƙarin farashin don kuwa bai zo a lokacin da ya dace ba.
Yanzu haka wasu jihohin dake faɗin ƙasar nan na shirin shirya zanga-zanga domin nuna rashin goyon bayansu da irin halin matsi da gwamnatin ta Buhari ta jefa rayuwarsu.