Gamayyar kungiyar masu tuka baburin adaidaita Sahu ta jihar Kano karkashin jagorancin Alhaji Mansur Tanimu ta umarci mabiya wannan kungiya da su janye yajin aikin da suka fara nan take.
Shugaban kungiyar Alhaji Mansur Tanimu wanda Dalhalhatu Shehu Usman ya wakilta yayin zaman tattauna yanda za a samo bakin zaren hulhu tsakanin ‘yan Adaidaita Sahu da Hukumar KAROTA ta gwamnatin jihar Kano, ya ce a dawo a cigaba da aiki kamar yanda aka saba.
Dalhatu Usman ya ce Abubuwan da suka cimma a wannan zaman sulhu su ne za a cigaba da biyan kudin da ake biya na Naira 100 kullum abunda suke korafi shi ne sabunta lamba wanda shima sabuntawar tana nan amma dangane da kudin za Mu rika biya shi ne muka rubutawa gwamna muna rokon ko dai a raba kudin ya zama ba lokaci guda za a biya ba.
Ya ce ko kuma a yanke wani abu daga cikin abun da za a rika biya ma’ana a rage shi ko kuma gwamnatin ta yafe shi.