Tsohon gwamnan jihar Neja, Mu’azu Babangida Aliyu, ya ce ba za a kawo karshen ta’addanci da tayar da kayar baya ba idan har dimbin ‘yan Nijeriya ba su da nagartaccen ilimi ba.
Babangida Aliyu ya bayyana hakan ne a yayin da yake jawabi a Cibiyar Taron da gidauniyar tunawa da Sir Ahmadu Bello ta shirya na shekarar 2021 a Abuja, inda tsohon Gwamnan ya tabbatar da cewa karancin ilimin ga mazauna yankunan da ‘yan ta’addan ke shiga suna aikata ta’addanci hakan na tauye yadda za su ba da bayanai ga hukumomin da abin ya shafa kan tattara bayanan sirri balle ma har a kai ga magance matsalar.
Babangida Aliyu ya ce; “Idan ba mu ilmantar da jama’armu ba, Boko Haram da sauran ta’addanci ba zai kare ba, saboda za a samu mutane masu son fafutukar neman hakkinsu a gareku (gwamnati), kuma suna ganin hakan daidai ne”, inji shi.
Babangida Aliyu, wanda har wala yau shi ne Shugaban kwamitin amintattu na gidauniyar, ya ce tun lokacin da gidauniyar ta fara bayar da tallafin karatu ga marasa galihu a arewa, ta ba da guraben karatu ga dalibai 800.