Kungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta mai taken (Global Community for Human Right Network) tace zata dauki matakin shari’a akan hukumar KAROTA matukar bata yi kokarin samar da daidaito tsakanin su da masu baburan Adai-daita Sahu ba.
Shugaban kungiyar Kwamared Karibu Yahya Lawan Kabara shine ya bayyana hakan a yayin zantawarsa da manema labarai a ofishin kungiyar dake unguwar Sharada Kwanar Freedom yau Talata.
Kwamared Kabara ya kara da cewar, kamata yayi shugaban hukumar lura da zirga-zirgar ababen hawa KAROTA ya samu damar zama da matuka baburan domin samun masalaha a tsakaninsu.
“A shirye muke wajen shigewa gaba dan nemawa dukkanin mutanen da aka dannewa hakki biyo bayan yajin aikin ‘yan Adaidaita Sahu ta hanyoyi daban daban, “inji Karibu Kabara.
A safiyar jiya Litinin 10 ga watan Janairun wannan shekara ta 2022 ne dai matuƙa baburan suka tsunduma yajin aikin sai baba ta gani, biyo bayan saɓunta lamba da hukumar KAROTA tace suyi, inda suka ce yin hakan an takura musu matuƙa, kuma ko a yau Talata ma suna cigaba da yajin ba ƙaƙƙautawa.
Daga karshe shugaban ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ɗin ya kara da ja hankalin gwamnatin jihar Kano da ta kara duba na tsanaki akan hukumar KAROTA, domin daukar matakin da ya dace kan sabunta rijistar yan Adaidaita Sahun, bisa irin halin damuwa da mutane da dama suka shiga biyo bayan yajin aikin.