Mabiya dariku a garin Zariya kamar yadda suka saba a duk shekara, sun gudanar da zagayen Maulidin fiyayyen halitta, Manzon Allah (SAW). Zagayen Maulidin wanda aka fara shi tunda safiyar yau Lahadi 10 ga watan Nuwamba wanda ya yi daidai da 13 ga watan Rabi’ul Awwal, ya samu halartar dimbin masoya Manzon Allah (SAW) na garin Zariya da kewaye.
Mabiya Harkar Musuluci a Nijeriya, wadanda aka fi sai da ‘yan Shi’a a karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Al-Zakzaky dake garin Zariya suna daga cikin wadanda suka shiga sahun masu zagayen Maulidin a bana kamar yadda suka saba a duk shekara.
Wakilinmu da ya shaida zagayen maulidin, ya ga yadda dubban daruruwan al’ummar Musulmi suka yi tururuwa wajen fitowa cikin murna da sabbin kaya cikin tsari, suna Ambato da rera wakar yabo ga Annabi (S).
Wakilinmu ya lura da yadda makarantun Islamiyyu sama da 300 ne suka halarci zagayen Maulidin, a yayin da akwai kabilu daban-daban wanda ya hada da Inyamurai da Yarabawa da suka kasance cikin sahun masu zagayen Maulidin (SAW).
Wadansu daga cikin masu zagayen sun taso ne tun daga Kofar Kuyan Bana har Fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau. Ya zuwa hada wannan rahoton, har zuwa karfe 6 na yamma, masu zagayen Maulidin ba su kammala ba.