By Abbas Yakubu Yaura
Mawakin Najeriya, Joshua Olonitan wanda aka fi sani da (Slim Joe), ya rasu bayan ya kwashe tsawon lokaci yana fama da ciwon koda.
Wani a bokinsa wanda ya kasance kuma abokin aikinsa Raymond Gbaji ne ya sanar da mutuwarsa a ranar 1 ga watan Janairu a shafin sa na Facebook.
Rahotanni sun ce Slim Joe ya rasu yana da shekaru 30 a duniya.
A shekarar da ta gabata ne dai aka ruwaito cewa mawakin na fama da matsalar gazawar gabobi.
Slim Joe ya shiga harkar waka ne bayan fitowar wakarsa mai suna ‘O ti Yan Yan’.
Ya fito da wakoki da yawa a ƙarƙashin tambarin sa na sirri, Yan Yan rikodin kuma ya ƙunshi manyan ayyuka kamar Don Jazzy da Iyanya.
Wasu daga cikin wakokinsa sun hada da: ‘Bless my hustle,’ ‘Packaging’ mai dauke da Don Jazzy da ‘Biliwo’ mai dauke da Iyanya.