Shahararren mawakin nan, David Adeleke, wanda aka fi sani da Davido, ya nuna soyayyar sa ga wata masoyiyarsa mace, a wani taron Lago.
Mawakin ta gwangwaje yarinyar da kyautar takalminsa da Naira miliyan biyu.
A lokacin da ya taka rawar gani a bikin Infinix VIP da aka yi a daren Lahadi, mawakin ya gayyaci yarinyar tare da kuma ya ba ta takalmansa.
Bayan ta karbi takalman ne ta dimauce saboda murna, inda ta zagaya cikin tashin hankali yayin da ta yi tsalle ta zagaya filin wasa, ta kwanta a kasa, ta rungume mawakin, inda daga baya ya umarci daya daga cikin masu taimaka masa ya ba ta Naira miliyan biyu.
Bidiyon da aka dauka lokaci ya yi ta yawo a yanar gizo, lamarin da ya sa masoya Davido da dama suka yi ta murnar mawakin saboda ayyukan alheri da ya yi.
Mawakin dai na daga cikin mawakan Najeriya, wadanda ludayin su ke kan dawo.