Shahararren mawakin gambarar nan na Amurka Lil Loaded ya riga mu gidan gaskiya yana da shekara 20 a duniya.
Lauyan mawakin mai suna Ashkan Mehryari ya ce matashin mawakin ya kashe kansa ne yayin da yake jiran wata Shari’a.
A shekara ta 2020 ne aka kama mawakin wanda asalin sunansa shine Dashwan Robertson bisa zargin kisan wani matashi mai shekara 18 mai suna Khalil Walker.
Kazalika a watan Fabrairu an zargi Lil Loaded da yankan rago wa wani matashi, lamarin da aka garkame shi a gidan maza gabannin yi masa Shari’a.
Lil Loaded ya yi suna a shafin YouTube inda a kowace rana yake samun mutane sama da miliyan 29 idan ya wallafa bidiyo a shafin nasa da ya samu sahalewa daga masana’antar nadar wakoki na Amurka.
Kawo yanzu dai a hukumance ba a gano dalilin sanadiyyar salwantar rayuwar mawakin ba, amma dai likitoci na ci gaba da gudanar da bincike.