Sama da mutane 70 da ake zargin ‘yan Boko Haram ne sun nutse a cikin kogi sakamakon harin bam da aka kai ta sama da rundunar Operation Hadin Kai a jihar Bornota jagoranta. in ji majiyoyi.
Daily Trust ta ruwaito cewa sojojin Najeriya tare da hadin gwiwar Civilian Joint Task Force (JTF) sun kashe mayakan Boko Haram sama da 20 a kauyen Sheruri da ke karamar hukumar Bama a ranar Alhamis.
Majiyoyi sun ce bayan harin Sheruri, wadanda suka tsere sun nutse a cikin wani kogi da ke kusa da kauyen Dipchari na karamar hukumar Bama a ranar Juma’a.
KARANTA WANNAN LABARIN: Limami Ya Mutu A Hanyarsa Ta Dawowa Daga Jana’iza
“Masu tada kayar bayan sun sha da kyar; sun yi asarar mayaka fiye da 70 a kusa da kauyen Dipchar. Da yawa ba a san inda suke ba yayin da muke magana,” inji majiyar tsaron.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa wakilin Majiyar Dimokuradiyya cewa, bayan faruwar lamarin, an ga maharan suna kwaso gawarwakinsu da dama a cikin kogin.
“A safiyar yau da misalin karfe 8:30 na safe, sun gudanar da jana’izar mayakansu sama da 50 a kauyen Dipchar kuma suna ci gaba da neman sauran ‘yan ta’addan.
Majiyar ta ce “Sun kwaso gawarwaki da dama daga cikin kogin amma har yanzu da dama daga cikin mayakan sun bace bat.”
Sai dai Babu wata sanarwa a hukumance daga babban hafsan sojin kasar nan kafin hada wannan rahoto amma yawancin mazauna yankin sun tabbatar da faruwar lamarin.
Rahotanni sun nuna cewa, Sojoji sun samu nasarori da dama kwanan nan a sassa da dama na kasar nan.
A WANI LABARIN KUMA: A Kwai Kimanin Sama Da Bindigogi Miliyan 6 A Hannun Fararen Hula — Rahoto
Makaman dai a cewar rahoton sun kai kashi 3.21 cikin mutum 100, yayin da jimillar bindigogi dubu 224,200 da dubu 362,400 ke hannun dokar soji da sauran jami’an tsaro, bi da bi.
Ana alakanta yawaitar kananan makamai da tabarbarewar tsaro a kasar, duk da kokarin da ake yi sau da dama, ciki har da amincewa da kafa Cibiyar Kula da Kananan Makamai ta Kasa da Gwamnatin Tarayya ta yi, domin dakile yaduwar shigo da bindigogi a cikin kasar.