‘Yan kwanaki kadan bayan cika shekaru takwas da sace ‘yan matan makarantar Chibok da ke Kudancin Jihar Borno, mayakan da ke da’awar kafa daular Musulunci a yammacin Afirka (ISWAP) sun sake awan gaba da wasu ‘yan matan shida daga yankin, inji rahoton Daily Trust.
A ranar 14 ga watan Afrilun 2014 ne mayakan Boko Haram suka kai farmaki makarantar sakandiren ‘yan mata ta gwamnati da ke garin Chibok, inda suka yi awon gaba da ‘yan mata 276 da ke shirin jarabawar kammala karatunsu na shekarar.
A ranar Larabar makon jiya ne aka gudanar da taron addu’o’in mabiya addinai a harabar makarantar ta GGSS Chibok a wani bangare na gudanar da bukukuwan tuna cika shekara takwas da sace mutanen da aka yi a shekarar 2014.
An kuma ce an kashe wani dan banga guda a sabon harin da aka kai wa al’ummar da ya faru a yammacin Lahadi.
An tattaro cewa rundunar ta ISWAP ce ta hau motocin da babura inda suka afkawa kauyen Yimir Mugza, kana suka bude wuta, lamarin da ya tilastawa mazauna kauyen tserewa cikin daji.
Wata majiyar tsaro ta ce maharan sun kashe wani dan banga dan shekaru 17 da haihuwa mai suna Godwin inda suka yi awon gaba da motoci hudu da kekuna uku da dabbobi da kuma kayan abinci.
Majiyar da ba za ta so a ambaci sunan ta ba saboda dalilan tsaro ta ce hudu daga cikin ‘yan matan da aka sace ‘yan gida daya ne.
A cewar majiyar, harin na baya-bayan nan ya kasance karo na bakwai da ‘yan tada kayar bayan suka mamaye al’ummar tun a shekarar 2014 da aka kwashe ‘yan matan 276 daga Chibok.
Har zuwa lokacin da aka buga labarin, majiyar ta ce, an kai rahoton lamarin ga hukumomin tsaro ko da an jibge wasu sojoji a yankin.
Awani labarin Kuma na daban
Gobara ta ƙone Wani Bene a Ilori
Wani Dogon Bene Mai hawa uku a ranar Talata ya ƙone a Ilori, Babban Birnin Jahar Kwara.
Gobarar ta faru ne a Igbala kusa da hanyar Filin Wasa a cikin garin Ilori.
Lamarin a cewar sanarwa daga bakin Mai Magana da Hukumar Kashe Gobara ta Jaha Hassan Hakeem Adekunle ya faru ne da misalin ƙarfe 7:50 a dalilin Wutar Lantarki.
Ya bayyana cewa Motocin Kashe Gobara sun gano cewa an sanya Dutsen Guga a jikin Soket a lokacin aikin ceton.
“Jami’an dake Kula da Kashe Gobara wanda ya Jagoranci Ceton, ya bayyana cewar duk Wutar Lantarki ta haddasa Gobarar, anga Dutse sanye a jikin Soket”, Inji Mai Magana da Yawun.
Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jahar Kwara Prince Falade John Olumuyiwa, yayi kira ga Mazauna garin dasu jefar da aƙidar barin wani abu a jikin Wuta kafin kwanciya.
Ya bayyana cewa wannan zai taimaka wajen magance Gobara a gidaje, tare da rage Afkuwar hakan.