Akalla jami’an gwamnatin jihar Borno guda biyar ne kungiyar ‘yan ta’adda ta ISWAP ta yi garkuwa da su.
A ranar yau Larabar ce aka tafi da wadanda lamarin ya rutsa da su, wadanda ke sa ido kan aikin hanyar Chibok zuwa Damboa.
Lamarin ya faru ne a kusa da Wovi, wani kauye mai nisa da Shelkwatar karamar hukumar Chibok.
Wata majiya ta shaida wa jaridar Daily Trust cewa daya daga cikin ma’aikatan da aka sace, direban motar ne ya tsallake rijiya da baya.
Wani babban jami’in jihar ya tabbatar wa majiyar Jaridar Dimokuradiyya faruwar lamarin, “Eh, abin bakin ciki ne kuma mun damu da wannan sabon lamari.”
“Samen ya zo mana da mamaki. Zan iya tabbatar muku da cewa an sace su da safiyar yau.”
Comments 1