Mayakan Taliban sun lakadawa mata masu zanga-zanga duka tare da harbin iska a ranar Asabar din nan, yayin da suka tarwatsa wata zanga-zangar da ba kasafai ake yin ta ba a babban birnin kasar Afganistan, kwanaki gabanin zagayowar ranar cika shekara ta farko da masu tsatsauran ra’ayin Islama suka koma kan karagar mulki.
Tun bayan kwace iko da kasar a ranar 15 ga watan Agustan shekarar da ta gabata, kungiyar Taliban ta dawo da koma bayan da mata suka samu a cikin shekaru ashirin na tsoma bakin Amurka a Afghanistan.
KARANTA WANNAN: https://dimokuradiyya.com.ng/kotun-akwa-ibom-ta-yanke-hukuncin-kisa-ga-wani-mutum-mai-mata-12-da-%c9%97iya-60/
Dimokuradiyya ta rawaito cewa, Kimanin mata 40 – masu rera “bread, work and freedom” – sun yi cincirindo a gaban ginin ma’aikatar ilimi a birnin Kabul, kafin mayakan su tarwatsa su ta hanyar harba bindigogi sama, in ji wakilin AFP.
Wasu mata masu zanga-zangar da suka fake a shagunan da ke kusa da wajen, mayakan Taliban sun fatattakie su tare da lakada musu duka.
Masu zanga-zangar dai na dauke da wata tuta mai dauke da “August 15 is a black day” ma’ana “15 ga watan Agusta bakar rana” yayin da suke neman hakkin aiki da kuma shiga harkokin siyasa.
“Adalci, adalci. Mun kosa da jahilci,” sun rera waƙa, da yawa ba sa sanye da mayafin fuska.
Zholia Parsi, daya daga cikin wadanda suka shirya wannan tattaki ta ce “Abin takaici, ‘yan Taliban daga hukumar leken asiri sun zo suka yi harbi a iska.”
“Sun tarwatsa ‘yan matan, sun yayyage tutocinmu tare da kwace wayoyin ‘yan mata da dama.”
Wasu ‘yan jaridar da ke ba da labarin zanga-zangar – gangamin mata na farko a cikin watanni – suma sun sha duka a wajen mayakan Taliban, kamar yadda wakilin AFP ya gani.
AFP/CHANNELS TV