Gwamnatin Jihar Legas ta ce ta samu rahotanni daga mazaje daban-daban har 88 da ke cewa matan su na azabtar da su a rayuwar aure.
Kwamishinar Harkokin Mata da Dakile talauci a Jihar Cecilia Bolaji Dada wacce ta bayyana haka a jiya Talata yayin wani taron yan jarida don murnar cika shekara guda na gwamnatin Jihar a kan mulki, ta ce wadannan korafe-korafe an same su ne tsakanin shekarar da ta gabata da kuma farkon watannin ukun wannan shekara.
Ta ce mazaje 46 ne a shekara ta 2020 suka kai rahoton yadda mazajen su ke azabtar da su, yayin sauran 43 kuma an same su ne a watanni uku na farkon wannan shekara, wanda jimilla ta kama mutane 89 kenan.
Kuma ta ce duk wadannan korafe-korafe har 89 fa kawai wadanda aka kai Ma’aikatar WAPA ne, ba ta haɗa da na ma’aikatar shari’a da kuma ofisoshin yan sanda ba.
To sai dai ta ce adadin azabar da maza ke gana wa matan su a jahar ta Legas ya ninka wadanda matan ke yi ninkin-ba-ninkin, domin a cewar ta a shekarar da ta gabata kawai an samu korafe-korafe har 664 daga matan da suka tsinci kansu a wannan yanayi.