By Ishaq Dabai
Mazauna garin Ado Ekiti, a ranar Juma’a, sun yi tir da hauhawar farashin Gas na dafa abinci a kwanakin nan, suna mai cewa yakamata gwamnati ta magance matsalar ci gaban da hakan.
Pst.Segun Adekunle ya shaida wa manema labarai cewa hauhawar farashin Gas ɗin girki yana da ban tsoro, musamman ganin cewa ba a kawo wasu dalilai na ƙarin ba kudin ba, sannan Ya bayyana yadda farashin yake inda yace yana iya tashi daga N3,000 zuwa N7,000 akan silinda mai nauyin kilogram 12.5 a cikin ‘yan watanni, yana mai cewa ci gaban ya kara wahalar da jama’ar Ado Ekiti, saboda a yanzu ya yanke shawarar amfani da itace da gawayi don dafa abinci a maimakon Gas.
“Dafa abinci da itace yana da haɗari ga lafiya,” in ji shi, duk da haka, ya koka.
Wata mazauniyar birnin Misis Bunmi Ajisafe, ‘yar kasuwa, ta nuna damuwa game da hauhawar farashin Gas na dafa abinci, tare da lura da cewa hauhawar ta kara tabarbarewar tattalin arzikin iyalinta.Ajisafe tace ta yi mamakin hauhawar farashin kayan masarufi a kwanakin nan, ba iya Gas kadai ba.
”Abin takaici ne da ba ku da tabbacin farashin na gaba da za ku hadu da shi lokacin da kuka je kasuwa.Gaskiya na damu da mamaki, na yi tunanin Najeriya kasa ce mai yawan iskar Gas, ”in ji ta.
Ta roki Gwamnatin Tarayya data sa baki cikin gaggawa, in ba haka ba zata iya komawa amfani da murhun kananzir, gawayi ko itace dan cigaba da dafa abinci.
Misis Tope Ogunfowokan, ma’aikaciyar gwamnati, tace har yanzu ‘yan Najeriya ba su gama murmure ba daga wahalhalun annobar cutar COVID-19 wanda ya gurgunta harkokin kasuwanci da dama kuma ya sanya mutane da yawa ba su da aikin yi.