Daruruwan mazauna kauyen Awo- Mmamma a karamar hukumar Oru ta Gabas ta jihar Imo sun tsere daga gidajensu bayan da rahotanni suka ce wasu ‘yan bindiga sun kashe jami’an soji da yammacin ranar Litinin, inda Kuma suka bayyana lamarin a matsayin abin takaici.
Wasu majiyoyi a yankin Awo-Mmamma sun shaida wa wakilin DAILY POST a ranar Litinin cewa, an yi ta yin kaura da dimbin jama’a, musamman matasa daga cikin yankin, saboda fargaba.
Da yake ba da labarin munin lamarin, ya ce wasu ‘yan Bata gari sun kai hari kan wasu sojoji a mahadar Ishieke da ke Awo Mmamma inda suka kashe daya daga cikinsu, suka kuma zarce zuwa Ihiala a jihar Anambra su Kai wani harin ramuwar gayya da sojojin suka kai yankin tare da yin Bankawa Gidan Mai, motoci, gidaje, otal da shaguna wuta.”
Wani shugaban al’ummar da ya nemi a sakaya sunansa ya ce, mumunan lamarin da ya faru a mahadar Ishieke Wanda Kuma ya janyo asarar dukiya ta miliyoyin Naira.
Ya ce, “Kamar yadda nake magana da ku yanzu, an kona gidaje da dama a daren nan. Yanzu muna cikin barazanar sojojin da suka fusata.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan, Micheal Abattam, ya umurci wakilinmu da ya tuntubi rundunar soji.
Sai dai ko da ya tuntubi Kakakin Rundunar ya ce zai dawo gare mu, amma har zuwa lokacin hada rahoton, bai dawo ba, inji Jaridar Daily Post