By Abbas Yakubu Yaura
Daruruwan mazauna garin Goma dake Jamhuriyar Dimokaradiyyar Kwango sun gudanar da zanga-zangar nuna adawa da isar jami’an tsaron kasar Rwanda a yankin.
Rikici ya barke tsakanin fusatattun matasa da ‘yan sandan yankin wanda ya yi sanadin jikkatar wasu da dama da kuma mutuwar wani dan sanda a ranar Litinin a garin Goma wanda shi ne babban birnin Kivu ta Arewa.
Jaridar Dimokuradiyya ta rawaito cewa Galibin masu gudanar da zanga zangar sun kafa shingaye a kan hanyoyi da dama inda suka toshe ababen hawa.
“A kasarmu, muna da sojoji da ‘yan sanda nagari, amma ba mu fahimci dalilin daya sa ‘yan Ruwanda za su zo su tsare mu a nan kasarmu ba, tun da Mobutu ne shugaban kasar nan bai taba sayar da kasar ba a yau mun kulla yarjejeniya da Tshisekedi da Rwanda don ‘yan sandan su zo nan, mun ki hakan,” in ji wani mai zanga-zangar.
“Mu a matsayinmu na ‘yan Kwango mun dade muna shan wahala, muna nuna rashin amincewa da zuwan ‘yan sandan Rwanda a kasarmu, mun ki saboda muna da ‘yan sandan mu,” in ji wani mai zanga-zangar.
‘Yan sandan sun tarwatsa masu zanga-zangar da barkonon tsohuwa da harsashi mai rai. An kashe dan sanda daya da wani mai zanga-zangar tare da jikkata wasu da dama, a cewar alkaluman wucin gadi.
A ranar Asabar, babban kwamishinan ‘yan sandan kasar Kongo ya musanta wannan zargi yana mai cewa babu ‘yan sandan waje da zai zo Goma inda ya danganta wannan zargin a matsayin karya.